- An sauya sunan jami’ar jihar Bauchi da ke Gadau zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU) domin girmama ɗan siyasar kuma dattijon ƙasa
- Gwamna Bala Mohammed ya sa hannu a kudirin sauya sunan jami’ar bayan majalisar dokokin Bauchi ta amince da shi
- Mataimakiyar shugabar jami’ar, Farfesa Fatima Tahir ta ce canza sunan ya ƙara nuna tasirin Sa’adu Zungur a ɓangaren ilimi a Bauchi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al’amuran yau da kullum
Jihar Bauchi – Gwamna Bala Mohammed ya amince da sauya sunan Jami’ar Jihar Bauchi da ke Gadau zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU).
Gwamna Bala ya rattaɓa hannu kan kudirin sauya sunan jami’ar bayan majalisar dokokin jihar Bauchi ta amince da shi.
Haka nan kuma majalisar gudanarwa ta jami’ar ta goyi bayan canza sunan jami’ar da wani taro da ta gudanar ranar Jumu’a, 14 ga watan Yuni, jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Mahukuntan jami’ar sun amince da sauya sunanta zuwa jami’ar Sa’du Zungur a zaman da suka yi ƙarƙaƙhin jagorancin shugaɓansu, Farfesa Ango Abdullahi.
Meyasa aka canja sunan Jami’ar Bauchi?
Shugaban jami’ar, Farfesa Ango Abdullahi ya ce sun amince da wannan sabon suna ne domin karrama marigayi Malam Sa’adu Zungur, dan kishin kasa kuma dan siyasa.
Ango ya jaddada muhimmancin girmama mutanen da suka taka rawar gani wajen gina al’umma da ƙasa baki ɗaya, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
A nata bangaren, mataimakiyar shugabar jami’ar (VC), Farfesa Fatimah Tahir, ta yaba da sauya sunan jami’ar jihar Bauchi zuwa jami’ar Sa’adu Zungur.
A cewarta, wannan wata alama ce da ke nuna ƙimar jami’ar wajen tafiyar da harkokinta a kan gaskiya da kuma bayar da ilimi mai inganci.
Farfesa Fatima ta ƙara da cewa sauya sunan ya nuna irin tasiri da gudummuwar da Sa’adu Zungur ke da shi a fannin ilimi a jihar Bauchi.
Gwamna Bala ya raba goron Sallah
A wani labarin kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya gwangwaje ma’aikata a jihar da abin alheri yayin da ake shirin Sallah.
Gwamna Bala ya raba kyautar N10,000 ga duka ma’aikatan jihar domin gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala.
Asali: Legit.ng